Taɓarɓarewar Tsaro: Muna Goyon Bayan Tsige Buhari – Dattawan Arewa

Ƙungiyar Dattawan Arewa ta bayyana matsayinta dangane da batun tsige Shugaban kasa da aketa cece kuce akai, inda ta bayyana goyon bayanta ga Majalisar ƙasa na daukar matakin tsige Buhari sakamakon gazawarshi wajen samar da tsaro a ƙasa.

Mai magana da yawun kungiyar Dattawan Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana hakan inda ya bukaci majalisa da ta tsige shugaba Muhammadu Buhari idan ba zai iya samar da tsaro ga yan kasa ba. Shugaban na fuskantar matukar matsin lamba ne sakamakon karuwar rashin tsaro a kasar.

Da yake magana a shirin Kakaaki, na gidan talabijin din AIT, ranar Litinin, Baba-Ahmed ya bukaci masu rike da mukamai da su fahimci halin da kasar nan ke ciki, su kuma yi wani abu na daukar mataki ba wai daukar alkawarurruka ba.

“Hanya daya da muke da ita shine yan majalisu su bibiya ayyukan wannan gwamnati, su fahimci inda shugaban kasa ya gaza, su fahimci inda ba wata hujja da za ta nuna cewa ana yin wani abu don daukar mataki, sannan su duba kundin tsarin mulki wanda yace babban aikin gwamnatin shine tsare rayuwar yan kasa da kuma tabbatar da walwala da jin dadin su.”

“Idan Buhari ya gagara haka, ni a gani na, in ya gaza haka a tsige shi. A wata shida da suka gabata, ko shekara biyu, me shugaban kasa ya yi don tsare kasar? Maganar gaskiya ba abun da aka yi sai dai ma koma baya wajen tsare rayuwar al’umma,” a cewar sa.

“Ko kuma, kamar yadda tsarin dimokradiyya ya bada dama, masu alhakin tsigewa, su tsige wanda suka gaza. Idan shugaban kasa ya gaza a tsige shi.

“Bamu da yan majalisu masu kishin kasa fiye da wasu tsirarun yan siyasa bare su gane cewa idan suka gaza, suma sun gaza. “Rashin iya mulki ya janyo mutanen da muka zaba muka aika Abuja suke tunanin su yi wa shugaban kasa aiki ba yan kasa ba.”

A cewar Baba-Ahmad, mataki na biyu shine yan kasa su taru su yanke matakin da ya kamata su dauka. Ya ce mataki na uku shine: “shugabannin da suka gane gazawar su da kansu suka san sune matsalar, suyi murabus da kansu saboda basu da abin da su iya a shugabanci.

Labarai Makamanta

Leave a Reply