Taɓarɓarewar Tsaro: Babu Dalilin Sulhu Da ‘Yan Bindiga – Jakadan Hayin Banki

An bayyana cewar babu wani dalili na kusa ko na nesa da zai sanya gwamnati a dukkanin matakai ta yi sulhu da ‘yan bindiga, domin babu wani ɗa mai ido da yin hakan zai haifar.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani Basarake a jihar Kaduna Jakadan Hayin Banki Alhaji Abdullahi Gambo Abba lokacin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a Kaduna dangane da ƙaruwar matsalar tsaro dake addabar Najeriya musamman yankin Arewacin kasar.

Gambo Abba wanda jigo ne a jam’iyya mai mulki ta APC ya ƙara da cewar abu ne wanda ba zai yiwu ba, ɗan ta’adda wanda ya saba karɓar miliyoyi a hannun jama’a da sunan kuɗin fansa sannan ya amince ya yi watsi da makamai ya koma rayuwarshi ta baya cikin talauci.

Basaraken ya nuna goyon bayanshi dangane da matakan da gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban ƙasa Buhari ta ɗauka ta bakin mai bada shawara kan harkokin tsaro Janar Babagana Mungono na cewar gwamnati ba za tayi sulhu da ‘yan bindiga illa ta yi maganinsu kawai.

“Idan muka dubi al’amuran sosai za mu ga cewar da akwai Jihohin da suka rungumi matakin yin sulhu da ‘yan bindiga, amma abin takaici kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba, Jihohi irin su Zamfara da Katsina”.

Abdullahi Gambo Abba ya kuma jaddada goyon bayanshi akan matsayar da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i ya dauka na cewar ba zai yi sulhu da ‘yan bindiga ba, inda ya tabbatar da cewa babu shakka wannan matsaya ta Gwamna ita ce mafita kawai.

Labarai Makamanta