Sun Shiga Hannu Bayan Kashe Yarinyar Da Suka Yi Wa Fyaɗe Ta Hanyar Jefata Ruwa

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, karkashin jagorancin Kwamishinan ‘yan sanda Alhaji Sanusi Buba ta yi nasara cafke, Mubarak Lawal, mai Shekaru goma sha shidda da haihuwa da Anas Ibrahim, mai shekara goma sha biyar da kuma Aliyu Mika mai shekara goma sha biyar dukkan su da ke kauyen Dutsen Dadi da ke cikin karamar hukumar Danmusa a Jihar Katsina, bisa zargin yiwa Safiya Basiru, ‘yar shekara goma sha ukku, wanda bayan kowane daga cikin su ya yi fasikanci da ita kuma suka jefa cikin wani tafkin, inda ta rasu cikin ruwa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isah ya yi baje kolin su a helkwatar rundunar da ke Katsina.

SP Gambo Isah ya kara da cewa sun yi wannan aika-aika ne a ranar 14/08/2020, inda suka yi wa Safiya Basiru a cikin gona, bayan kowane ya yi lalata da ita suka jefa ta wani gulbi, kuma ta rasu. An samu gawarta a gulbin, aka kai ta asibitin garin Danmusa inda aka tabbatar da rasuwarta.

Gambo Isa ya ce a cikin bincike yan sanda, dukkansu sun amsa aikata lafin. Kuma ana cigaba da binciken.

Labarai Makamanta