Sulhu Ya Kamaci ASUU Ba Yajin Aiki Ba – Shugaban Kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci kungiyar malaman jami’o’i da sauran kungiyoyin ma’aikata da su rungumi sulhu da gwamnati tare da gudun yajin aiki a matsayin hanyar neman a biya musu bukatu.

Buhari ya bayyana hakan ne a taro na 74 na yaye dalibai a jami’ar Ibadan a ranar Alhamis 17 ga watan Nuwamba shekarar da muke ciki ta 2022.

Shugaba Buhari ya samu wakilcin farfesa Abubakar Rasheed ne a taron, wanda shine babban sakataren hukumar jami’o’i ta kasa (NUC).

Buhari ya kuma yaba da kokarin gudunarwar jami’ar Ibadan bisa kare martabar jami’ar a idon duniya.

Ya kuma yaba da kokarin jami’ar wajen yaye Ɗalibai masu digiri na farko masu nagarta da ke sanya kasa alfahari a ciki da wajen kasar nan.

Yajin aiki na taba tattalin arziki da nagartar karatu, ya kuma bayyana cewa, akwai bukatar ladabtarwa da tabbatar da halaye na gari a dukkan jami’o’in kasar nan domin ciyar da kasar nan gaba. Ya shaida cewa, ya kadu da yadda kungiyoyin jami’o’i a kasar nan suka daura damarar fada da gwamnati a wannan shekara ta 2022.

Shugaban ya ce sabanin da ke tsakanin gwamnati da malaman na da matukar tasiri mai muni ga tattalin arzikin kasar nan, musamman duba da yadda hakan ke shafar zangon karatun dalibai.

Labarai Makamanta