Sulhu Ne Kaɗai Hanyar Magance Matsalar Tsaro -Farfesa Usman Yusuf

An bayyana cewar zaman sulhu a tsakanin gwamnati da waɗanda ake kira ‘yan bindiga ita ce hanya guda da ta saura wajen samar da tsaro a ƙasa, inda aka bukaci shugabanni a yankin Arewa da su yi kokarin zama da wadannan ‘yan bindiga domin samun nasarar da ake nema.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin tsohon Shugaban Hukumar inshorar lafiya ta ƙasa Farfesa Usman Aliyu lokacin da yake jawabi a cikin shirin”Baƙonmu Na Mako” da gidan Talabijin na Liberty Abuja ya yi dashi.

Farfesa Usman wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka rufawa Dr. Ahmad Gumi baya a ziyarar da ya kai dazukan Zamfara da Kebbi domin ganawa da ‘yan bindiga, yace ko kaɗan matakin amfani da ƙarfin Soji ba zai haifar da nasara ba sai dai ƙara dagula al’amurra.

“Abubuwan da na gani a ziyarar da muka kai wa ‘yan bindiga abu ne dake sanya damuwa, tabbas akwai ƙorafin da suke yi na anyi watsi dasu da rashin nuna kulawa da halin da suke ciki, wanda hakan ya ke tunzura su suke ɗaukar matakan ƙwatar kai”.

Farfesa Usman Aliyu ya tabbatar da cewar yana da kyakkyawan yakini muddin Gwamnati ta kusanci waɗannan ‘yan bindiga ta hanyar yin sulhu dasu tabbas za su miƙa makamansu da rungumar tsarin zaman lafiya. Inda ya nuna damuwar shi akan aniyar wasu gwamnoni musamman na yankin Arewa maso yammacin Najeriya da ke sukar matakin sulhu da ‘yan Bindigar da cewar su sake tunani.

Dangane da rikicin kabilanci da ya kunno kai a sashin Kudancin Najeriya musamman Jihohin Yarbawa dangane da kisa da korar Fulani da ake yi a yankin, Farfesa Usman ya gargadi shugabanni da yin gaggawar ɗaukar mataki domin daƙile yiwuwar ballewar rikicin kabilanci a ƙasar wanda zai haddasa zubar da jini da kisan ƙare dangi, kamar yadda aka samu a kasashen Laberiya da Ruwanda.

Labarai Makamanta