Sulhu: El Rufa’i Zai Gana Da Shugabannin Kwadago Yau A Abuja

Gwamnatin tarayya ta gayyaci gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, da shugabannin kungiyar kwadago NLC zuwa wajen taron gaggawa data shirya domin yin sulhu a tsakanin su, da niyyar kawo karshen rikicin dake tsakanin bangarorin biyu.

Gwamnatin ta sanya ranar yau Alhamis 20 ga watan Mayu domin tattaunawar sulhu tsakanin ɓangarorin biyu a babban Birnin tarayya Abuja.

Wannan na cikin ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi domin dakatar da yajin aikin da kungiyar ke yi gaba ɗaya da kuma rikicin dake tsakanin gwamnatin Kaduna da ƙungiyar ƙwadagon kan sallamar ma’aikata a jihar Kaduna.

Gwamnatin ta gayyaci ɓangarorin biyu ne ta ofishin ministan kwadugo, Chris Ngige, domin ta shiga tsakani. An shirya yin zaman sulhun ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe a ofishin ministan Kwadago na ƙasa ranar yau Alhamis a Abuja.

Waɗanda aka gayyata zuwa wajen taron sulhun sun haɗa da; Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i tare da manyan jami’an gwamnatinsa, da kuma shugaban kungiyar kwadago NLC, Ayuba Waba, tare da manyan shugabannin ƙungiyar.

Labarai Makamanta