Sulhu Da ‘Yan Bindiga: Shekau Ya Soki Lamirin Dr. Gumi

Shugaban kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram, Abubakar Shekau, ya soki lamirin fitaccenmalamin addinin Islama da ke zaune a Kaduna, Sheikh Dr. Ahmad Gumi, saboda tattaunawa da ‘yan bindiga da yake faman yi.

Kwanan nan Dr. Gumi ya shiga rangadi zuwa maboyar ‘yan bindigan dake dauke da muggan makamai a dazuka domin kulla yarjejeniyar zaman lafiya da masu tada kayar bayan.

Zagayen malamin ya jawo maganganu daban-daban a tsakanin ‘yan Nijeriya, inda mutane da yawa, ciki har da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, suka yi Allah wadai da matakin.

Amma a cikin wani faifan murya da ya kai tsawon awa 1 da mintuna 55, wanda aka samo daga jaridar Daily Nigerian, Shekau ya ce Gumi na daga cikin wadanda suke yin barna da ganganci.

“Haba Ahmad Gumi! Haba Ahmad Gumi, yanzu kana yawo, kana tattaunawa da Fulani, kuma kana tunanin kana bautawa Allah. “Saboda kawai ana ce maka Dokta ko Sheikh?Kaiconka Ahmad Gumi,” .

Ya kawo maganar sura ta 7 aya ta 175 na Alkur’ani, shugaban ‘yan ta’addar ya ce game da Gumi: “Kuma ka ba su labarin (ya Annabi) wanda muke bai wa ayoyin Mu, sai ya yi watsi da su, sai Shaidan ya kama shi, kuma ya zama karkatacce.”

Shekau ya kuma zargi Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani na Najeriya, wanda malamin addinin Musulunci ne, saboda ya shiga gwamnati a karkashin tsarin dimokiradiyya.

“A gare ku (Gumi) da wasu irin su Pantami, menene ma minista, huh? Kuma har yanzu malami ne? Ku tambayi kanku! Ya ku malamai masu dandana dandanon mulki da iko, ku tambayi kanku,” in ji shi.

“Dukkanku kun san dimokiradiyya akidar yahudawa da kiristoci ne, me yasa ba ku bar gwamnati ba? “Duk da sanin gaskiya, kuna amfani da Alkur’ani wajen wa’azin dimokiradiyya. Me ya sa haka?”

Labarai Makamanta