Sukar Gwamnatin APC: Ganduje Ya Kori Hadimi

Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya kori hadimin sa Salihu Tanko Yakasai daga ci gaba da yi masa aiki bayan ya ragargaji jam’iyyar APC da gwamnatin Buhari tare da yin tir da salon mulkin Buhari.

Kwamishinan yada labarai na Jihar Kano Garba Muhammad wanda ya saka wa takardar korar hannnu ya ce Salihu Tanko bai iya banbance ra’ayin sa da matsayinsa na hadimin gwamnan da yake sukar shugaban sa ba.

” Tunda bai gamsu da salon mulkin da yake ciki ba, babu amfanin ya ci gaba da yi wa wannan gwamnati aiki.

Bayan haka gwamna Ganduje ya gargadi ma’aikatan gwamnati su rika iya wa bakunan su.

Mahaifin Salihu Tanko, Tanko Yakasai ya tabbatar wa manema labarai cewa ba garkuwa da dan sa aka yi ba, jami’an tsaro na farin kaya ne, SSS suka arce da shi Abuja.

” Ba sace Salihu aka yi ba jami’an SSS ne suka tafi da shi Abuja.

Tun bayan awon gaba da Salihu da SSS suka yi da safiyar Asabar aka rika zargin ko masu garkuwa da mutane ne suka arce da shi.

Salihu Tanko ya ragargaji Buhari da jam’iyyar APC a lokacin da ya rubuta cewa jam’iyyar sa, APC ta gaza, ta yaudari ‘Yan Najeriya ne rashin iya kawo karshen matsalar rashin tsaro da ame fama da shi a kasar.

Salihu ya ce ” Da ma fa talakawan Najeriya sun zabe mu ne domin a kawo musu karshen matsalar rashin tsaro da kasar ke fama dashi amma kuma maimakon sauki tabarbarewa da muni abin yayi.

” Ace wai a kullum aka tashi sai an kwashi mutane da sunan an yi garkuwa da su, abu kamar almara. Idan ba zaka iya ba ka hakura mana ka tattara ka yi tafiyar ka. Abin ya muni matuka.

Idan ba a manta ba, ranar Juma’a mahara suka kwashe daliban makarantar sakandare a Jangebe, jihar Zamfara.

Ba wannan ne karon farko da Salihu Tanko, ke ragargazar gwamnatin Buhari ba. A baya da ya yi irin haka gwamnan Kano Ganduje ya dakatar da shi da ga ci gaba da yi masa hidima, sai dai daga baya ya dawo da shi.

Labarai Makamanta