Sukar Gwamna: Lamidon Adamawa Ya Tuge Rawanin Dan Majalisar Fada

Rahotanni daga Yola babban birnin Jihar Adamawa na bayyana cewar mai martaba LamidonAdamawa, Muhammadu Barkindo, ya warware rawanin da ya naɗa wa Umar Mustapha saboda ya caccaki gwamna Ahmadu Fintiri.

An ruwaito cewa Umar Mustapha wanda jigo ne a jam’iyyar APC ya caccaki gwamnan Adamawa ne bayan ya baiwa sarakunan gargajiyar Jihar Kyautar sababbin motoci.

Masarautar Adamawa ta bayyana cewa Umar Mustapha bai cancanci ya cigaba da rike mukamin, ‘Mukaddas Adamawa’ biyo bayan abin da ta kira raini ga gwamnati.

A wata sanarwa da ya fitar, ya sokin Lamirin gwamnan kan kyautar manyan motocin da ya yi.

“Bai kamata a kashe miliyan N200m wajen siyo sabbin motoci ga sarakuna ba yayin da masu jiran Fansho ke mutuwa sanadiyyar yunwa.”

Bayan haka ne Lamiɗo Barkindo, a wata sanarwa ta hannun sakataren masarauta, Khalil Kawu, yace an tube rawanin Umar Mustapha. Wani sashin sanarwan masarautar yace: “Mai martaba sarki ya bayyana cewa Umar Mustapha bai cancanci rike mukamin sarauta ba sakamakon caccakar da ya yi wa gwamna kan motocin da aka baiwa sarakuna a jihar.”

Sarkin ya kuma nuna tsantsar damuwarsa kan cewa Mustapha ya gaza fahimtar kyakyawan kudirin da gwamnati ta yi wa Sarakunan gargajiya na wannan kyauta.

Labarai Makamanta