Sukar Buhari: Bugaje Ya Sha Matsa A Hannun DSS

Rahotanni sun tabbatar da cewa DSS ta yi nasarar damke Dr. Usman Bugaje ne a game da wata hira da ya yi da gidan talabijin na AIT, inda ya soki Gwamnatin tarayya ƙarkashin jagorancin Shugaban kasa Buhari da yin Allah wadai da salon shugabancin Shugaban.

Wasu makusantan Bugaje sun ce ya kai kan shi hedikwatar DSS a birnin tarayya Abuja ne da kimanin karfe 10:00 na safiyar jiya bayan an aika masa gayyata.

Hukumar DSS ta tura wa tsohon ‘dan majalisar Jibiya/Kaita da goron gayyata ne bayan an yi hira da shi sau biyu a gidan talabijin na AIT a Abuja, inda ya taƙarkare wajen sukar Buhari da jam’iyyar APC mai mulki.

Bayan kimanin sa’o’i takwas ana yi masa tambayoyi, jami’an tsaron sun saki ‘dan siyasar. Da alama Bugaje ya bar ofishin DSS ne ana daf da za a sha ruwa.

“Usman Bugaje ya bayyana sau biyu a wani shiri da gidan talabijin na AIT ta shirya makwanni biyu da su ka gabata, sai ya samu gayyata daga DSS cewa ana nemansa a ofishinsu domin ya yi karin haske kan wasu abubuwa da ya fada a shirin da aka yi.”

Majiyar ta kara da cewa: “A ranar Laraba kenan daa kimanin karfe 10:00 na safe, Dr. Bugaje ya hallara a ofishin SSS da ke Abuja, inda aka tsare shi.”

Rahotanni sun bayyana cewa sai kusan karfe 7:00 na yamma aka bada belin shugaban Arewa Research and Development Project (ARDP), sannan ya samu, ya tafi gida.

Bugaje wanda ya rike Sakatare a tsohuwar jam’iyyar ACN, ya na cikin manyan jiga-jigan APC, amma daga baya sai aka ji ya koma sukar gwamnatin Muhammadu Buhari.

Kafin yanzu Dr. Bugaje ya nemi takarar gwamnan jihar Katsina a 2007 da 2015, amma bai yi nasara ba. A 2016 ya ki karbar kujerar da Buhari ya ba shi.

Labarai Makamanta