Sukar Atiku: PDP Ta Ba Obasanjo Wa’adin Kare Kai

Babbar Jam’iyyar adawa taPDP, ta bukaci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi karin haske kan kalaman da ya furta kan dan takarar shugaban kasarta, Atiku Abubakar na cewa ya yi kuskure wurin zabensa a matsayin mataimakinsa a 1999 ba tare da ɓata lokaci ba.

A cewar PDP idan tsohon shugaban kasar bai yi karin haske kan kalaman da aka danganta da shi ba cikin awa 48, jam’iyyar za ta fada wa yan Najeriya ainihin ko wanene Obasanjo.

Da ya ke magana a taron manema labarai a Kaduna a ranar Litinin, Shugaban Kwamitin amintattu na PDP, Sanata Walid Jibrin, kuma ya bayyana cewa an kafa kwamiti don ganawa da gwamnan Rivers Nyesom Wike kan batun mataimakin shugaban kasa. Ya ce jam’iyyar za ta warware matsalolinta.

A cikin sanawar da aka ce tsohon shugaban kasar ne ya fadi game da Atiku da jaridu suka wallafa, Walid Jibrin ya ce shi da PDP su na girmama tsohon shugaban kasar. Amma, cikin gaggawa ya kara da cewa za su yi matukar takaici idan har da gaske ne shi ya furta maganganun da aka danganta da shi.

“Ina son kira ga tsohon Shugaba Obasanjo ya fito fili ya maimaita abin da ya ce. Ko an yi kuskuren rahoto abin da ya fada ne ko kuma hakan ya ke nufi. “Duk da cewa bai karyata abin da aka ruwaito ba, za a iya tsammanin rahoton gaskiya ne, amma idan bai fito fili cikin awa 48 ya bayyana menene gaskiya ba, za ka ji sako daga gare mu kuma ba ni da zabi sai dai in fasa kwai in fada wa duniya ko wanene Obasanjo.

“Babu shakka akwai yiwuwar Obasanjo har yanzu yana fushi da Atiku duk da ya taimake shi amma ya datse masa damar yin tazarce na uku, Alhaji Abubakar Atiku dan takarar shugaban kasar mu ne kuma ina tabbatar maku insha Allahu zai zama shugaban kasa a 2023.”

Labarai Makamanta