Hukumomin sojin kasar Sudan sun kaddamar da wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan rigingimun da suka haddasa kashe-kashe a jihar Blue Nile da ke kudancin kasar.
Shafin intanet na kafar yaɗa labaran ƙasar wato Suna ya ruwaito cewa rikicin ya yi sanadiyyar rayuka kusan 200 tare da raba dubbai da muhallansu.
Kashe-kashen ya biyo bayan rikici tsakanin Hausawa da wasu ƙabilun ƙasar, wanda ya ƙara zafafa a makon da ya gabata.
Mai magana da yawun sojin kasar kanar Nabil Abdullah ya ce kwamitin da aka kafa zai yi bincike tare da sake duba yanayin tsaro a kasar.
Hukumomin ƙasar sun ce sun kaddamar da sabuwar rundunar soji ta musamman da za ta yi aiki a jihar domin kula da rikici tsakanin ƙabilu.
You must log in to post a comment.