SSS Na Zargin Emefiele Da Daukar Nauyin Ta’addanci

Hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) a bisa wasu takardun bincinke da kotu ta samu ta zargi Gwamnan Babban Bankin Najeriya , Godwin Emefiele da tallafawa ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba da kuma mambobin haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB).

Kafofin yada labaran Najeriya, sun ruwaito a watan Disamba 2022, yunkurin Hukumar tsaro ta farin kaya  na neman samun umarnin wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, na kama  Emefiele kan wasu zarge-zarge da suka hada da samar da kudaden ta’addanci.

Babban alkalin babbar kotun tarayya, John Tsoho, bayan ya saurari tawagar lauyoyin SSS, ya ki amincewa da bukatar bayar da umarni kama Gwamnan Banbban bankin Najeriya Emefile.

Alkalin ya ki amincewa da bukatar a hukuncin da aka yanke ranar 9 ga watan Disamba 2022, saboda rashin bin ka’ida a tsarin da hukumar SSS ta dauka a cikin bukatar ta.

Daga cikin zargin da  hukumar SSS ta yi masa,akwai batun zagon kasa ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, da bayar da tallafin ta’addanci, da taimakon ta’addanci, da kuma aikata wasu laifukan da suka shafi tattalin arziki da ke da nasaba da zagon kasa ga tsaron kasa Najeriya.

Hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) ta kuma zargi Emefiele da aikata laifuka da suka shafi reshen babban banki wato  CBN, NSRAL, da kuma shirin tallafawa manoma na Anchor Borrowers Programme na babban bankin kasa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply