Sokoto: Za A Bude Makarantar Da Aka Kashe Deborah

Labarin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewa za a bude kwalejin ilmi ta Shehu Shagari da ke garin Sokoto biyo bayan rikicin da ya faru a watan Mayu, inda aka hallaka Deborah Yakubu matashiyar da ta yi ɓatanci ga Annabi.

Rahotanni sun bayyana cewar a ranar 5 ga watan Agusta shekarar 2022 aka yi na’am da a sake bude wannan makarantar horas da malamai ta Shehu Shagari da ke garin na Sokoto.

Bayanai sun tabbatar da tun da aka babbaka Deborah Yakubu a sakamakon kalaman batanci da tayi a dandalin WhatsApp, aka bada umarnin a rufe wannan makaranta.

A ranar 8 ga watan Agusta 2022 wanda zai kama Litinin za a koma daukar darasi a makarantar Mahukuntar kwalejin ilmin ne suka bada wannan sanarwa. Magatakardar kwalejin da ke jihar Sokoto, Gandi Asara ya tabbatar da cewa majalisar da ke kula da makarantar ta amince a koma aiki a mako mai zuwa.

Hukumar kwalejin ta sanar da dalibai za su biya N1000, sannan za su yi rantsuwar cewa za su zama masu hali na kwarai yayin karatunsu a makaratar.

Labarai Makamanta