Sokoto: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane Da Dama A Kauyen Rabah

Kawo yanzu ana cigaba da tattara gawawakin mutane da dama wadanda ‘yan bindiga suka yiwa kisan gilla a kauyen Rarah dake cikin karamar hukumar mulkin Rabah ta jahar sokoto da tsakar ranar yau dinnan kamar yadda muka baku labarin dazu.

Daga cikin wadanda aka cinto gawawakin su Akwai ‘yan sakai da kuma Limamin masallacin jumu’ah na 2 dake kauyen Liman Shehu Rarah da wasu mutane.

‘yan ta’addan sun tabka Babbar barna a kauyen da har yanzu ba’a ida kammala tantancewa Ba.

Amma sai dai, bayan sun kashe mutane haka ma sun da duniyoyin dama dabbobin Al’umma.

Yan ta’addan dai sun shiga ne da misalin karfe 3 na ranar yau litinin sun yi musayar wuta tsakanin su da ‘yan sakan kauyen

Labarai Makamanta