Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya buƙaci Rundunar Sojin Nijeriya, da ta sake yin dubi akan dabarun yaƙin da take amfani dashi.
Tambuwal ya bayyana haka a lokacin da Babban Hafsan sojin Najeriya Laftanar-Janar Faruƙ Yahaya ya kai mashi ziyara, a gidan Gwamnatin jahar a ranar 18 ga watan Oktoba na shekarar 2021.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hulɗa da jama’a Onyema Nwachukwu ya sanyawa hannu aka fitar dashi a ranar Litinin.Gwamna Aminu Waziri Tambuwal
Gwamnan yace harin da ƴan ta’adda suka kai a ƙauyen Goronyo abin baƙin ciki ne, a saboda haka akwai buƙatar dake akwai na sake yin dubi akan dabarun yaƙi a shiyyar domin magance sake faruwar hakan.
“Ya kuma jaddada buƙatar dake akwai na ƴan ƙasa da jami’an tsaro dasu gano waɗanda suka aikata ta’addancin a cikin al’umma, inji sanarwar.
Ya kuma yi kira ga al’umma da kada su goyi bayan duk wani mai goyon ƴan ta’adda, musamman masu sanar dasu bayanan sirri da kuɗaɗe.
Yayi kira ga Gwamnatin Tarayya data ƙaro jami’an tsaro, domin baiwa hukumomin tsaro damar gudanar da yaƙi cikin sauƙi.
A jawabin shi, Babban Hafsan sojin Najeriya Laftanar-Janar Faruƙ Yahaya ya yabawa Tambuwal na irin cigaba da bayar da goyon bayan shi ga Rundunar sojin Najeriya, inda ya buƙace shi daya cigaba da hakan.
Ya bada tabbacin cewa, Rundunar sojin Najeriya bazata baiwa gwamnati kunya ba, a ƙoƙarin ta na inganta yaƙin da akeyi a yankin Arewa maso Yamma.
You must log in to post a comment.