Sokoto: Kwamishinan Da Ya Lashe Shekaru 14 Bisa Mukami Ya Rasu

Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar Kwamishin noma a jihar, Alhaji Arziƙa Tureta, ya rigamu gidan gaskiya bayan shafe shekara 14 a ofis matsayin Kwamishina mafi dadewa a muƙami.

Tureta ya rasu ne yana da shekara 62 a duniya bayan yayi fama da doguwar rashin lafiya. Mai magana da yawun ma’aikatar noma, Muktar Dodo Iya, shine ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai (NAN) haka a Sokoto.

Alhaji Tureta ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Litinin a asibitin koyarwa na jami’ar Usman Ɗan-Fodio dake Sokoto (UDUS), ya rasu ya bar mata biyu da ‘yaƴa bakwai.

Marigayi Tureta ya taɓa riƙe kujearar ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Tureta a majalisar dokokin jihar Sokoto. Daga baya ya zama ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Bodinga/DangeShuni/Tureta a majalisar wakilai ta tarayya Hakanan kuma, Tureta yayi aiki a matsayin kwamishina a zamanin mulkin tsohon gwamnan Sokoto, Aliyu Wamako, na tsawon shekara takwas.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, ya sake naɗa shi a matsayin kwamishinan noma, inda ya shafe shekara shida kafin rasuwarsa.

Labarai Makamanta