Sokoto: An Shiga Makoki Sakamakon Rasuwar Ɗiyar Sardauna

‘Yar Sardaunan Sokoto Sir Ahmadu Bello ta biyu Aishatu Ahmadu Bello ta rasu tana da shekara 75.

Marigayiyar tsohuwar matar Marafan Sokoto ce Alhaji Ahmad Danbaba.

Jaridar DailyNagerian ta ruwaito cewa Hassan Dan baba ne ya tabbatar da rasuwar mahaifiyar ta sa a ranar Juma’a, yana cewa ta rasu ne a wani asibiti ne a Dubai bayan fama da wata matsagaiciyar rashin lafiya.

Tuni dai aka gudanar da sallar jana’izarta a birnin Sokoto kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Mahaifinta Sir Ahmadu Bello shi ne Premier arewa na farko kuma na karshe wanda ya rike mukamin daga shekarar 1954 zuwa 1966 lokacin da aka kashe shi a wani juyin mulkin soji.

Labarai Makamanta