Sokoto: An Damke Tsohon Sojan Da Ke Taimakon ‘Yan Bindiga

Hukumar NDLEA mai yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta ce ta kama wani tsohon soja mai shekara 90 da zargin yi wa ‘yan fashin daji safarar ƙwayoyi a Jihar Sokoto.

Wata sanarwa ta ce an kama Usman Adamu ne ranar Laraba, 3 ga watan Agusta a garin Mailalle na Ƙaramar Hukumar Sabon Birni.

“An kama shi da tabar wiwi mai nauyin 5.1kg,” a cewar kakakin NDLEA Femi Babafemi.

Kazalika a ranar Alhamis, hukumar ta kama wata mota a JIhar Zamfara maƙare da ƙwayar Diazepam 50,000 a kan hanyarta ta zuwa Sokoto daga birnin Benin na Jihar Edo, wanda ta ce mallakar wani ne mai suna Umaru Attahiru.

A wani binciken na daban, NDLEA ta damƙe wani fasto mai suna Anietie Okon Effiong da duro uku na ƙwayar crystal methampetamine – wadda ake kira Mkpuru Mmiri a Najeriya.

Kayan da NDLEA ke zargin an shiga da su ne daga Indiya, an kama su yayin da ake shirin kai su wani wuri a birnin Legas lokacin da aka tare motar da ke ɗauke da su.

Labarai Makamanta