Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ministar al’amuran mata ta Najeriya Mrs Pauline Tallen, ta buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da mai ɗakinsa Aisha Buhari, da su sa baki a batun soke zaɓen fidda gwani na gwamna da jam’iyyar APC ta gudanar a jihar Adamawa.
Mrs Tallen ta yi kiran ne a lokacin wani taron ministoci da kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN ya shirya a Abuja babban birnin ƙasar, ta kuma ce matakin soke zaɓen abu ne da ba za a lamunta ba.
Ta ƙara da cewa ”Soke zaɓen ‘yar takararmu ta gwamna mace ɗaya tilo a Adamawa abu ne da ba za a amince da shi ba”.
Ta kuma yi kira ga ilahirin al’umma da su goyi bayan ‘yan takara mata a zaɓukan 2023, domin samun ci gaban ƙasa.
You must log in to post a comment.