Sojoji Sun Fitar Da Hotunan ‘Yan Ta’adda Da Ake Nema Ruwa A Jallo

Hedkwatar tsaro ta Najeriya, a ranar Litinin ta fitar da sunayen kwamandojin yan ta’adda 19 da ke adabar yankunan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya a kasar, inda ta ayyana nemansu ruwa a Jallo.

Hedkwatar tsaron ta ce za ta ba da tukwicin Naira miliyan 5 ga duk wani dan Najeriya da ya bada bayanan yadda za a kama yan ta’addan, ta bukaci al’umma su tuntube ta a wannan lambar 09135904467.

Ta ce hakan ya zama wajibi ne domin cigaba da kawar da abokan gaban, inda ta kara da cewa hakan yunkuri ne na dawo da zaman lafiya gaba daya a kasar, musamman yankin arewa dake fama da fitinar ‘yan Bindiga.

Sunayen yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo da Direkta na sashen watsa labarai na hedkwatar tsaro, Manjo Janar Jimmy Akpor ya fitar sune:

1- Sani Dangote – Asalinsa: Kauyen Dumbarum . Karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara. 2- Bello Turji Gudda – Asalinsa: Kauyen Fakai na Jihar Zamfara. 3-Leko – Asalinsa: Kauyen Mozoj, Karamar Hukumar Mutazu ta jihar Katsina. 4-Dogo Nahali – Asalinsa: Kauyen Yar Tsamiyar Jno. Karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina. 5-Halilu Sububu – Asalinsa: Kauyen Sububu a karamar hukumar Maradun na jihar Zamfara. 6-Nagona – : Asalinsa: Kauyen Galadima a Isa Loa na jihar Sokoto. 7-Nasanda – : Asalinsa, Kauyen karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara. 8-Isiya Kwashen Garwa – Asalinsa: Kauyen Kamfanin Daudawa na karamar hukumar Faskari, Jihar Katsina. 9-Ali Kachallaa da aka fi sani da Ali Kawaje – Asalinsa: Kauyen Kuyambara da ke karamar hukumar Danaadau Maru na jihar Zamfara. 10-Abu Radde – Asalinsa: Kauyen Varanda da ke karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina. 11-Dan-Da – Asalinsa: Kauyen Varanda da ke karamar hukumar Batsari na jihar Katsina. 12-Sani Gurgu – Asalinsa: Kauyen Varanda da ke karamar hukumar Batsari ta Jihar Katsina. 13-Umaru Dan Najeriya – Asalinsa: Kauyen Rafi. Garin Mada a Gusaulaga. 14- Nagala – Asalinsa: Karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara. 15-Alhaji Ado Aliero – Asalinsa: Kauyen Yankuzo da ke karamar hukumar Tsafe na jihar Zamfara. 16-Monere – Asalinsa: Kauyen Yantumaki , karamar hukumar Dan Musa na jihar Katsina. 17- Gwaska Dankarami – Asalinsa: Kauyen Shamushele da ke karamar hukumar Zuri na jihar Zamfara. 18- Baleri – Asalinsa: Karamar hukumar Shinkafi na jihar Zamfara. 19-Mamudu Tainange – Asalinsa: Kauyen Varanda a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Labarai Makamanta