Siyasar Kano: Yau Kotu Za Ta Raba Gardama

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar a yau Talata ne ake sa ran Kotun Ɗaukaka Ƙara za ta yi zaman sauraron ƙarar rikicin shugabanci a jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Kano tsakanin Gwamna Abdullahi Ganduje da ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau.

Ɓangaren Gwamna Ganduje ne ya ɗaukaka ƙarar bayan ya sha kaye a shari’o’i biyu da suka gabata, inda yake neman a soke shugabancin Ahmadu Haruna Zago, wanda ke samun goyon bayan tsohon Gwamna Shekaru, sannan a bayyana Abdullahi Abbas a matsayin halastaccen shugaba.

A wata shari’ar ta kotun tarayya na baya, kotun ta bayyana cewa ɓangaren Ganduje ba shi da hurumin neman a kori ƙarar saboda ya riga ya ɗaukaka ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara, saboda haka ne kuma ta yi watsi da buƙatarsu.

Rikicin APC a Kano ya samo asali ne tun bayan gudanar da tarukan jam’iyyar a matakin mazaɓu da jiha, abin da ya haddasa aiwatar da taruka biyu ƙarƙashin Sanata Ibrahim Shekarau da kuma ɓangaren gwamnatin Kano.

Labarai Makamanta