Siyasa: Tinubu Ya Kaddamar Da Manufofin Takarar Shi

Alkawura 10 da Bola Tinubu ya yi

1. Gina Najeriyar da matasa za su samu ayyukan yi tare da albashi mai tsoka domin jin dadin rayuwa.

2. Samar da kaya da ayyukan da ake bukata. Najeriya za ta rika samar da arziki, a maimakon kasancewa ci-ma-zaune.

3. A rika fita da arziki daga Najeriya, a rage yawan kayan da ake shigowa da su daga kasashen ketare.

4. Cigaba da taimakawa manoma ta hanyar tsare-tsaren aikin gona da za su sa al’umma ta koshi da abinci.

5. Zamanantar da abubuwan more rayuwa ta yadda tattalin arzikin kasa zai cigaba daidai gwargwado.

6. Tallafawa matasa a bangarori masu tasowa irinsu tattalin arzikin zamani, nishadi, al’adu da yawan bude ido.

7. Rage talauci ta hanyar horas da jama’a ta yadda za su samu arziki domin yara su daina kwana da yunwa.

8. A raba wutar lantarki domin mutane su samu haske wajen gudanar da ayyukansu da jin dadin zama a gida.

9. Kawo tsare-tsaren da za su taimaka wajen ganin kiwon lafiya, ilmin zamani da mallakar gidaje bai gagara ba.

10. A fito da tsare-tsare na musamman da za su kawo karshen ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran ta’adi.

Labarai Makamanta