Siyasa: Shugaban Majalisa Ya Gargaɗi Matasa Kan Zaɓen PDP

Labarin dake shigo mana daga Jihar Gombe na bayyana cewar Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya roki matasan jihar da na ƙasa baki ɗaya kada su sake kuskuren amincewa da PDP.

Lawan ya yi wannan furuci ne ranar Lahadi a wurin taron shirin koyar da sana’o’i da sanatan Gombe ta arewa ya shirya, domin inganta rayuwar Mata da Matasa a jihar.

Shugaban babbar majalisar ƙasar ya bayyana cewa tsawon shekaru 16 da PDP ta kwashe kan madafun iko, babu wani tsayayyen aikin cigaba da ta kawo wa ƙasa, face koma baya ta kowane fanni.

A cewar sanatan, zai zama babban abin dana sani da kuma takaici ga matasan Najeriya ace PDP ke jagorantar su domin ko shakka babu sai an yi nadamar faruwar hakan.

“Ba abin da PDP ta tsinana tsawon shekara 16, sun kashe dukiyar ƙasa ba tare da yin wani aikin cigaba ba. Bai kamata matasa su sake yarda da jam’iyyar PDP ba Jam’iyya ce ta macuta da Mayaudara.”

Shugaban sanatocin ya ƙara da cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya nuna kwarewa da salon mulki kuma ya gwangwaje yan Najeriya da romon demokaradiyya. Sanata Lawan ya bayyana cewa shugaba Buhari bai taɓa hutawa na dakika ɗaya ba tun lokacin da ya karɓi ragamar mulkin kasar nan a 2023.

“Muna ƙara gode wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, shine jagoran jam’iyya na ƙasa, wanda ya shugabance mu tun daga 2015 zuwa yau.

“Shugaban ya nuna bukatar gyara ƙasar nan, shugaban ƙasa bai taba hutawa na dakika ɗaya ba.”

Labarai Makamanta