Siyasa Ce Ta Sa Aka Tumɓuke Ni Daga Sarauta- Wakilin Birnin Bauchi

A wani martani da ya yi, Wakilin Birnin Bauchi Alhaji Abdullahi ya yi zargin cewa Gwamna Bala Mohammed na da hannu a dakatarwar saboda ya ki shiga jam’iyyar PDP bayan ya bar Jam’iyyar PRP inda a maimakon haka ya koma tsohuwar Jam’iyyarsa ta APC.

“Lokacin da na fice daga PRP gwamnan ya nemi na hade da shi a PDP amma na fada cewa zan koma APC saboda jam’iyata ce kuma mutanen da suka yi rashin adalci a kanmu ba su nan,” in ji shi.

Sai dai a martanin da ya bayar mai ba Gwamnan Bauchi shawara kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya kira zargin mara tushe.

Ya ce dalilin dakatar da Abdullahi shi ne kamar yadda ya bayyana a wasikar dakatarwa daga masarautar – rashin girmamawa ga sarki, majalisar masarauta da kuma masarautar gargajiya.

“Me ya sa bai bayyana batun gwamnan da ya nemi ya koma PDP ba har zuwa yanzu? “Yana da damar shiga kowace jam’iyya kuma babu wanda zai ci zarafinsa saboda zabin jam’iyyarsa, gwamnan ba shi da wata alaka da dakatarwar da aka yi masa kuma ya kamata ya je ya fuskanci majalisar masarautar,” in ji Gidado.

Abdullahi ya shaida wa Daily Trust cewa dakatarwar na da nasaba da siyasa saboda “an hana ni da sauran mukarrabai na shiga gidan Gwamnati a lokacin da ake yi wa gwamnan gaisuwar Sallah a ranar Asabar.”

Tuni dai Abdullahi ya yi ikirarin a ba shi damar yin bayani kafin majalisar ta yanke hukunci. “Kwamitin ya dauki matakin ne ba tare da jin bangare na ba don rashin adalci saboda jami’an tsaro sun hana ni da mukarrabai na mu kadai shiga gidan Gwamnati, lamarin da ya tilasta min saukowa daga kan doki na da kuma takawa zuwa wurin taron.”

Abdullahi ya kara da cewa duk da tsoma bakin da wasu jami’an gwamnati suka yi a bakin kofar, “jami’an tsaron sun dage cewa akwai umarni daga sama cewa kada su bari ni da tawaga ta mu shiga gidan gwamnati. A cewarsa bai yi mamaki ba saboda “Gwamna Bala Mohammed ya gaya mini cewa shi da kansa zai nuna rashin amincewa da sarautata ta gargajiya ta Wakilin Birni a gaban Sarkin Bauchi wanda ya yi daidai da lakabin babban yayansa na Wakilin Bauchi; Alhaji Adamu Muhammad.

Labarai Makamanta