Siyasa Ba Za Ta Hana Ni Harkar Fim Ba – Sani Danja


Fitaccen Jarumi a Masana’antar finafinai ta kannywwod Sani Musa Danja ya bayyana cewar Siyasa da wasu harkoki da ya ke yi, ba za su hana shi fitowa a fim ba.

Jarumin ya bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Dimukaradiyya dangane da Maganar da a ke yi a Kan sa cewar a yanzu ya fi mayar da hankalin sa a Siyasa fiye da fim da aka San shi da shi tun asali, in da ya ke cewa.

“Duk wanda ya sanni da harkar fim ya sanni Kuma ta dalilin sa ne duniya ta sanni duk wani abu na rayuwa da na samu duk ta dalilin fim ne don haka babu yadda za a yi na bar harkar fim”.

Ya ci gaba da cewa “Ko ita Siyasar ai Sai da na fito a fim na yi suna sannan hakan ya ba ni damar shiga Siyasar a lokacin mulkin Jonathan, wanda a lokacin ne mutune suka ga na shiga cikin Siyasa sosai. Kuma bayan Siyasa ai Ina tallan kamfanoni kamar Glo da sauran manyan kamfanoni da kungiyoyi na duniya, duk hakan bai sa na daina fim ba saboda shi fim sana’ata ne da aka sanni da shi, don haka babu yadda za a yi na bar fim”.

Daga karshe ya yi Kira ga Gwamnati da ta bayar da goyon baya ga masu harkar fim, saboda harka ce da miliyoyin mutane su ke samun aikin yi a cikin ta wadda yin hakan zai sa mutane su samu aikin yi su rabu da zaman jiran aiki, domin dogaro da Kan su.

Labarai Makamanta