Ɗan takarar jam’iyyar APC mai mulki Bola Ahmed Tinubu, ya taya abokin hamayyarsa na PDP Atiku Abubakar murnar cika shekara 76 da haihuwa.
A ranar Juma’a ne tsohon mataimakin shugaban ƙasar kuma haifaffen Jihar Adamawa da ke arewacin ƙasar ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar tasa.
“Ina taya Atiku Abubakar murnar ranar haihuwarsa ta 76,” in ji Tinubu cikin wani saƙon Twitter. “Ina yi masa fatan alheri.”
Wannan ne karo na shida da Atiku zai yi takarar shugaban ƙasa bayan ya yi rashin nasara a 1993, da 2007, 2011, da 2015, da kuma 2019.
A ranar 25 ga watan Fabarairu mutanen biyu za su fafata a babban zaɓen da ‘yan Najeriya za su zaɓi shugaban ƙasa da gwamnoni da ‘yan majalisar jiha da na tarayya.
You must log in to post a comment.