Siyasa: Atiku Na Zawarcin Gwamna Wike

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa a yammacin ranar Alhamis, 4 ga watan Agusta 2022 ne aka yi wani zama domin ayi sulhu tsakanin Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas.

An yi wannan zama ne a gidan tsohon Ministan tarayya a Najeriya, Farfesa Jerry Gana. Haduwar ‘dan takaran shugaban kasar da gwamnan na Ribas na zuwa ne jim kadan bayan kwamitin amintattu na BoT sun yi wani zama a Abuja.

BoT wanda sune kwamitin amintattu masu bada shawara a PDP sun sa baki a rikicin Atiku Abubakar da mutanen Wike wanda zai iya kawo cikas a babban zaɓen shekarar 2023 dake tafe.

Wannan ne karon farko da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar ya kebe daga shi sai Wike a tsawon watanni tun bayan zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP.

Baya ga haka, Atiku Abubakar da Nyesom Wike ba su fitar da wani jawabi a game da wannan haduwa ba. Kawo yanzu dukkaninsu ba suce uffan ba.

Wasu jagororin jam’iyyar PDP da suka san yadda taron ya kasance, sun shaidawa ‘yan jarida cewa an fara samun nasara daga zaman da ‘yan siyasar suka yi.

Labarai Makamanta