Shugabancin Kasa: Wajen Allah Na Ke Nema – Tinubu

Rahotanni daga Jihar Legas na bayyana cewar jigon jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, yace Allah ne mai bada mulki ga wanda yaso kuma a lokacin da ya so, saboda haka shi a wajen Allah yake nema.

Tinubu ya yi wannan furucin ne a Legas ranar Lahadi, yayin da ya sake haɗuwa da abokanan siyasarsa da ɗumbin mgoya bayansa a wurin liyafar maraba da kuma addu’a, wanda gwamna Sanwo-Olu ya shirya masa.

Taron liyafar ne na farko da Tinubu ya halarta tun bayan dawowarsa daga birnin Landan, ranar Jumu’a da daddare, inda ya shafe watanni uku.

Ana hasashen dai Bola Tinubu, na ɗauke da kudirin neman takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen dake tafe na shekarar 2023 karkashin APC.

Jigon jam’iyyar APC yace a koda yaushe idan Allah ya baka dama, to yana tsammanin ka yi amfani da wannan damar wajen kyautatawa mutane. Yace yaji daɗin wannan taron na yi masa addu’a musamman yadda yan Najeriya suka rinka masa fatan alkairi lokacin da baya ƙasa.

“Duk addu’ar da yan Najeriya suke mana, tana tasiri akaina kuma na ɗauke ta da matukar muhimmanci. “Ina cikin matukar farin ciki a halin yanzu, Allah ke bada rayuwa kuma shi kaɗai ne ke ɗaukar ran mutum.”

“Kuma Allah da kansa yace, idan na baka wani mulki to na baka wata dama ce a rayuwa; ni kadai zan iya kwace wa daga hannunka idan baka yi abinda ya dace ba.”

Tsohon gwamnan jihar Legas ya ƙara da cewa Allah ne ya raya kowa har ya kawo zuwa lokacin da yake tsaye a gaban masoya. “Allah ne ya raya mu zuwa yau har ga shi ina tsaye a gabanku cikin koshin lafiya. Yau rana ce ta farin ciki da zamu mika godiya ga Allah.”

Labarai Makamanta