Shugabancin Kasa: Tinubu Ne Mafita A Najeriya – Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Sokoto na bayyana cewar Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya faɗa wa mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, cewa ya shiga yaƙin neman zaben Bola Tinubu ne saboda abu uku.

Buhari ya bayyana haka ne yayin da ya jagoranci tawagar kamfen ɗin shugaban kasa na APC zuwa fadar Sarkin Musulmi da ke Sakkwato domin neman tabarruki.

Shugaban ƙasa ya ce tawagar yakin neman zaben ta ziyarci fadar Basaraken ne domin neman goyon bayan Sultan kuma ya zabi shiga cikin kamfen ne bisa dalilai uku.

A jawabinsa, shugaɓan kasan ya ce shi da Bola Tinubu sun jima tare da juna a matsayin abokai tsawon shekaru 20, sannan abu na biyu ya yi abun a yaba lokacin yana gwamnan Legas.

“Dalili na uku shi ne Tinubu ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na APC a sahihi kuma ingantaccen zaɓe, bisa haka ya zama halastaccen ɗan takara a jam’iyyata.” Daga nan kuma ya bukaci mai Alfarma Sarkin Musulmi da ya goyi bayan Tinubu, wanda Sultan da kansa ya kira da, “Jagaban duniya.”

“Na zo nan ne na roki ka marawa dan takararmu baya kuma na san cewa zaka ci gaba da goyon bayanmu,” inji Buhari.

Tun da fari, mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar APC, Bola Tinubu, ya faɗa wa Sarkin Musulmai cewa ya shiga tseren kujera lamba ɗaya ne domin ya ci nasara.

“Babbar daraja ce zuwa nan musamman tare da rakiyar mai girma shugaban ƙasa muka kawo ziyara fada. Kun riga kun sani amma bari na maimaita, mun zo nan ne domin a gabatar ni a matsayin ɗan takarar APC.” “Mun san cewa baka tsoma baki a siyasa amma dole mu girmamaka idan muka shigo garin na yin kamfe.”

Labarai Makamanta