Shugabancin Kasa: Peter Obi Ne Zabi Na – Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya fito karara ya nuna goyon bayansa da dan takarar jam’iyyar Labour Peter Obi, a daidai lokacin da ake tunkarar babban zaben kasar da za a yi awatan Fabirairu.

Obasanjo ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya yi wa take da “Kirana ga ‘yan Najeriya musammam matasa.”

Tsohon Shugaban ya ce babu daya daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar da yake ba shi da kashi a jikinsa, amma idan za a kwatantasu ta fuskar ilimi da bin ka’ida da kuma irin ci gaban da za su iya kawowa Najeriya to Obi ya sha gaban kowa.

“Babu wanda ba shi da kashi a gindinsa cikin duka ‘yan takarar amma in zaka kwatantasu ta fuskar halayya mai kyau da fahimtar lamura da ilimi da mayar da hankali kan aiki Peter Obi ne ya fi cancanta.

Labarai Makamanta