Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban Ć™asa Muhammadu Buhari ya shawarci ‘yan kasar a wannan sabuwar shekarar 2023 da aka shiga, su dage wajen kishin kasa da fatan ganin kasar ta ci gaba ta fuskar hadin kai da fatan ci gaba.
Cikin sakonsa na sabuwar shekara da ya aika a jiya, Shugaba Buhari ya ce 2023 shekara ce da za a kara mayar da hankali kan harkokin tsaro da bunkasa tattalin arziki da kuma yakin da cin hanci.
Buhari wanda ya yi maraba da suka da yabon da ‘yan Najeriya ke yi masa, ya ce ya yi iya abin da zai iya ga mutanen kasar, yayin da yake fatan duk shugaban da zai zo ya dora daga inda ya tsaya, domin ciyar da Najeriya caga.
Ya ce dole yan Najeriya su dauki ragamar tabbatar da zabukan da za a yi a 2023 an yi su babu cuta babu cutarwa.
Ya kuma shawarci ‘yan kasar da su kiyaye da tayar da hankali a lokutan zabe, su kuma kiyaye daga duk wani dan siyasa da zai nemi su yi hakan.
You must log in to post a comment.