Shugabancin Kasa: Kungiyar Fulani Ta Saya Wa Jonathan Fom

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a yayin da babban zaben shekarar 2023 ke cigaba da karatowa, wata kungiya karkashin ‘kungiyar fulani’ ta saya wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan fom din takarar shugaban kasa kan tsabar kudi naira miliyan N100.

Hotunan da TVC News ta wallafa a shafinta na Twitter ya nuna wasu cikin shugabannin kungiyar dauke da fom ɗin na takarar shugabancin ƙasa a Jam’iyya mai mulki ta APC.

Idan za a iya tunawa a watan Afrilu 2022, wasu mutane sun yi tattaki zuwa ofishin tsohon shugaban kasa Jonathan, suna bukatar ya fito ya yi takarar shugaban kasa a 2023.

Mai magana da yawun kungiyar, Mayor Samuel, wanda shine jagoran ‘Youth Compatriots of Nigeria’ ya ce: “Wasu da suka ce mana za su iya yin aikin a shekarar 2015 sun yaudare mu.

“Yanzu mun gane gaskiya, karkashin mulkin Jonathan, albashi mafi karanci zai iya siya maka buhun shinkafa. Yanzu me muke da shi a yau? Muna rokon tsohon shugaban kasa Jonathan ya yafe mana, mun gane kurenmu, muna so ya dawo ya karasa abin da ya fara.”

A martaninsa, Jonathan ya ce na san kun ‘zo ne domin ku nemi in fito takara, ba zan iya fitowa ba a yanzu domin har yanzu akwai wasu abubuwa da ke tafiya.

“Kuna kira in fito a zabe mai zuwa. Ba zan iya cewa zan fito takara ba. Ana tuntuba, ku jira ku gani. Muhimmin abin da za ku yi shine ku nemi wani da zai yi aiki tare da matasa.”

Labarai Makamanta