Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babban daraktan yakin neman zaben Atiku/Okowa a Anambra, Professor Obioro Okonkwo, ya ce akalla jam’iyyu 10 ne suka janye takara don marawa dan takarar PDP, Atiku Abubakar da mataimakin sa, Ifeanyi Okowa, a babban zaben shugaban kasa na 2023.
Okonkwo ya bayyana haka ga yan jarida jim kadan bayan kammala tattaunawar kwamitin yakin neman zaben daya gudana a babar hedikwatar kamfen a Akwa, ranar Juma’a.
Ya ce jam’iyyun adawa guda goma ne suka janye takara don goyon bayan takarar Atiku/Okowo, saboda sun san PDP ce zata lashe jihar da kuma Kudu maso Gabas kamar yadda ta saba kuma Anambra ita ce kan gaba a yankin; Abia, Enugu, Imo da Ebonyi duk sun shirya don a dawo da Najeriya hayyacin ta.
Ya ce sunyi ganawar ne don tabbatar da shirye-shiryen karshe kafin ranar zabe, ”Muna da yakinin yin nasara a Anambra. Mu mutane ne masu daraja wanda muka fuskanci meye siyasa da kuma kyakkyawar dimukradiyya.
”Baya ga dubban yan jam’iyyar adawa da suka dawo PDP a Anambra tun bayan da muka fara kira don ceto kasar nan, wasu jam’iyyu 10 sun karbi Atiku Abubakar da Ifeanyichukwu Okowa a matsayin yan takarar shugabancin kasa da mataimaki.”
”Muna da kwarin gwiwa a yunkurin mu na ceto Najeriya, alkawarin tabbatar da kasa daya, farfado da tsaro da tattalin arziki, da kuma sauran muhimman alkawura da Atiku yayi wa yan Najeriya, musamman Kudu maso Gabas.
”Don haka, zamu tabbatar sun yi nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa, kamar ko yaushe jam’iyyar PDP zata ci gaba da yin nasara a Anambra.” Kwamitin ya kuma bada tabbacin cewa halin kuncin da Najeriya ke ciki a yanzu zai zama tarihi a satin farko da Atiku ya kama aiki a matsayin shugaban kasa, saboda zai kawo tsarin da al’umma zasu amfana.
You must log in to post a comment.