Shugabancin Kasa: Ina Da Tabbacin Tinubu Zai Kai Najeriya Tudun Mun Tsira – Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce zai ci gaba da yi wa ɗan takarar jam’iyyarsu ta APC kamfe, Bola Ahmed Tinubu, don ya zama “shugaban ƙasa na gaba”.

Da yake magana a gaban dubban magoya bayansu a Jihar Nasarawa ranar Asabar, Buhari ya ce ya yi imanin Tinubu zai sadaukar da kansa ga Najeriya wajen

“Kamar yadda Tinubu ya faɗa cikin jawabinsa, na san shi fiye da shekara 20, kuma zan ci gaba da taya shi yaƙin neman zaɓe,” in ji Buhari cikin wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar.

“Ɗan ƙasa ne jajirtacce kuma na yi imanin zai sadaukar da kansa wajen yi wa Najeriya aiki.”

Kalaman nasa na zuwa ne kwana biyu bayan wasu jiga-jigai a APC sun yi zargin cewa wasu manya daga cikin jami’an gwamnatin ta Buhari na adawa da takarar Tinubu.

A cewar Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, masu adawar ba sa son APC ta yi nasara ne saboda ɗan takarar da suka mara wa baya a zaɓen fitar da gwani bai yi nasara ba.

Labarai Makamanta