Shugabancin Kasa: Hatsari Ne Yin Tikitin Musulmi Da Musulmi – Masu Ruwa Da Tsaki

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC sun yi kira ga shugabancin jam’iyyar da Kungiyar Progressive Governors da su tsaya neman mataimakin ‘dan takarar shugabancin kasa kan Kiristocin arewa kawai.

Hakan ya biyo bayan cece-kuce da ya yi yawa kan tikitin Musulmi da Musulmi wanda ya janyo maganganu daban-daban a kwanakin da suka gabata.

A yayin jawabi a wani shiri na shagalin bikin ranar damokaradiyya, Shugaban Kungiyar masu ruwa da tsakin APC na kasa, Aliyu Audu, ya bayyana bukatar watsi da duk wani abu da zai sa a dauko mataimaki Musulmi domin tabbatar da cigaban hadin kan kasar nan.

“Dalilin da yasa muka ankare da cewa kada addini ya zama madogara wurin zaben shugaba. Halin da kasar nan ta tsinci kanta a ciki yasa muka yanke wannan shawarar, matukar sun damu da rayukanmu da makomar ƙasar.

“A yau, kasar mu ta rabe a bangaren kabilanci da addini kuma ba za mu iya zuba ido a wannan abu mai muhimmanci ba. “Wannan ne dalilin da yasa muke tunanin dole a saka APC a hanya yayin zaben mataimakin ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar.

Audu ya ce, kin bin wannan shawarar zai assasa wutar rabuwar kan talakawa kuma ya kawo rabewar kai. Kamar yadda yace, Najeriya tana bukatar shugabanci nagari, wanda zai iya zuwa daga shugaba Musulmi ko Kirista.

Labarai Makamanta