Shugabancin Kasa: APC Ta Fara Tantance ‘Yan Takara

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC mai mulki na aikin tantance masu neman takarar shugabancin kasar a karkashin tutar jam`iyyar.

Da farko dai jam`iyyar ta tsayar da ranar Talatar da ta gabata a matsayin ranar tantacewar, amma sai ta dage ba tare da bayyana dalili da kuma sabuwar ranar da za ta yi aikin ba.

Ana aikin tantancewar a otal din Transcop Hilton a Abuja

Jumullar mutum 23 ne ake sa ran cewa za su halarci tantancewar.

Rahotanni na cewa ana sa ran tantance mutum 11 a ranar Litinin, sannan kuma sauran 12 kuma a talata.

Wannan duk na zuwa ne bayan da jam’iyar ta APC ta ɗage zaɓen fitar da gwanin da ya kamata ta gudanar 29 da 30 ga watan Mayu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply