Shugabanci: Buhari Ka Ji Tsoron Allah – Sheikh Gombe

Fitaccen Malamin addini Sheik Kabiru Gombe ya yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ji tsoron Allah a irin mulkin da yakewa Nijeriya da al’ummarta.

Malamin ya bayyana haka ne a wajan Tafsirin AlQur’ani wanda yake gabatarwa a Kaduna ofishin Manara TV a wannan wata na Ramadan.

Sheik Kabiru Gombe ya ce “Muhammadu Buhari kiwo Allah ya baka na Nijeriya kuma dole sai ya tambayeka yadda ka tafiyar da kasar nan.

Ya ce “kai sani cewa ranar tashin kiyama Allah zai tsaida kai gabansa ka fadi irin adalcin da ka yi wa ‘yan Kasarka”.

Ya ce “a wannan rana babu mataimakin shugaban kasa, babu sakatren Gwamnati, babu shugaban ma’aikata kuma babu wadanda ke take maka baya, haka za ka yi bayanin yadda ka tafiyar da kasa”.

Related posts