Shugaban Zambia Na Shan Suka Kan Yawan Tafiye-Tafiye

Shugaban kasar Zambia na shan suka daga ‘yan hamayya saboda yawan tafiye-tafiye zuwa kasashen waje

A jiya Laraba Mista Hichilema ya yi bulaguronsa na tara zuwa kasar waje tun bayan da ya hau Mulki a watan Agusta.

Tafiyar tasa ta baya-bayan nan ta kwana biyu ce, zuwa Afirka ta Kudu inda zai tattaunawa da takwaransa Cyril Ramaphosa tare da halartar wani bikin kaddamar da littafi.

Sai dai jam’iyyar hamayya ta masu ra’ayin gurguzu ta Socialist ta tuhumi tafiyar tasa bayan da aka bayyana ganawarsa da Mista Ramaphosa a matsayin ziyarar gaisuwa.

A lokacin da bai zama shugaban kasa ba, yana dan hamayya, Mista Hichilema yana yawan sukan wanda ya gada Edgar Lungu a kan yawan tafiye-tafiye kasashen waje.

Labarai Makamanta