Shugaban ‘Yan Sanda Ya Yi Wa Manyan ‘Yan Sanda Garambawul

Babban Baturen ‘Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya sauyawa manyan jami’an ‘yan sandan yankin kudu maso gabas wurin aiki a matsayin hanyar shawo kan matsalar tsaro a yankin.

A cikin wata takardar sanarwa da Frank Mba, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya ya ya fitar a ranar Juma’a, yace sauyin ya fara aiki ne nan take.

Daga cikin wadanda aka sauyawa wurin aikin akwai Monday Bala Kuryas, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Anambra.

Mataimakan kwamishinonin ‘yan sanda 16 lamarin ya shafa kuma hakan ya gangara har zuwa jihohin kudu maso kudu na kasar nan.

Labarai Makamanta