Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya shigar da ƙudirin neman jingine umarnin kotu da ya ɗaure shi wata uku a gidan yari, yana mai cewa bai raina umarnin kotun ba.
Cikin ƙorafin da ya gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya a Abuja ranar Alhamis, shugaban ‘yan sandan ya ce ba a ƙarƙashin shugabancinsa aka aikata laifin da kotun ta yi hukunci a kansa ba kuma “ba a saɓa wa umarnin kotu ba”.
A makon nan ne Babbar Kotun Tarayya ta ba da umarnin kama babban sufeton tare da garƙame shi tsawon wata uku saboda saɓa umarnin kotun da ta ce a mayar da Patrick C. Okoli kan aikinsa bayan an tilasta masa yin ritaya ba bisa ƙa’ida ba.
“Ya tabbatar da cewa an ba da umarnin ne a Nuwamban 2018 da kuma Janairun 2019 ga sufeto janar na ‘yan sanda na lokacin, ba a kansa ba wanda shi ne yake riƙe da muƙamin a yanzu,” a cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Juma’a.
IGP Usman Baba ya ƙara da cewa sufeto janar na lokacin ya bi umarnin kotun, inda ya rubuta wasiƙa ga hukumar kula da harkokin ‘ya sanda don a mayar da Mista Okoli bakin aiki.
You must log in to post a comment.