Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ‘yan Sanda na ƙasa Alkali Baba Yayi Umarnin Gaggauta Bincike da Gurfanar da ‘Dan Sandan da ya Halaka wata Lauya a ranar Litinin, Disamba 26, 2022 a garin Legas.
Usman Baba Alkali, Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya ya yi tir da kisan Bolanle Raheem, wata lauya da jami’in ‘dan sanda dake aiki da caji ofis din Ajiwe dake Ajah ta jihar Legas ya halaka washegarin ranar Litinin.
IGP Alkali Baba Yayi Umarnin Gaggauta Bincike da Gurfanar da ‘Dan Sandan da ya Halaka Lauyar domin fuskantar hukuncin da ya dace dashi.
You must log in to post a comment.