Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya umarci kwamishinan ‘yan sandan jihar Osun, Olaleye Faleye da ya bincike zargin cin zarafin wata sifetan ‘yar sanda mai suna Bamidele Olorunsogo da DCO din ta Ajayi Matthew yayi a Ode-Omu ta jihar.
Wannan na zuwa ne bayan bidiyon dake nuna shaidar mugun dukan da aka yi wa Bamidele ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani.
A bidiyon, Bamidele ta zargi abokin aikinta a ofishin ‘ya sanda na Omu a jihar Osun da cin zarafinta tare da bata mata suna. ‘Yar sandan ta zargi cewa Matthew ya bukaci ta zama budurwarsa amma ta ki amincewa saboda tana da aure, sai dai Matthew ya cigaba da bata mata suna inda daga bisani ya lakada mata duka.
Tace: “Mene ne laifina? Ya fara dukana har ta kai ga ya cire min kaya. Ku kalla kirjina, kafaduna da ko ina, duk raunika ne. Sunansa Ajayi Matthew. Ya bukaci mu kulla alaka amma nace a’a saboda ina da aure. “Daga nan ya fara bata min suna inda yake ikirarin cewa dama shi saurayina ne, wanda ba hakan bane.”
Duk kokarin da aka yi na jin ta bakin Matthew kan wannan zargin ya gagara saboda ya ki daukan kiran da aka dinga masa.
Sai dai, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, yayin da aka tuntubesa yace hedkwatar na jiran rahoton bincike daga rundunar ta jihar Osun kafin daukar matakin da ya dace.
You must log in to post a comment.