Shugaban Turkiya Na Ziyarar Kwanaki Biyu A Najeriya

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya fara wata ziyarar kwana biyu a Najeriya, inda ake sa ran zai gana da takwaransa Shugaba Muhammadu Buhari da kuma ƙulla yarjejeniyoyi tsakanin ƙasashen biyu.

Wata sanarwa da babban mataimaki na musamman kan hakar yaɗa labarai ga shugaban Najeriya, Mallam Garba Shehu ya fitar ta ce Erdogan da mai ɗakinsa Emine sun isa Najeriya ne daga Angola, kuma bayan kammala ziyarar, ana sa rai za su isa ƙasar Togo.

Ta ce Najeriya na ɗaukar Turkiyya a matsayin wata babbar aminiya kuma tana yi wa wannan ziyara kallon wani muhimmin al’amari a dangantakar ƙasashen biyu.

Labarai Makamanta