Shugaban Tsagerun Yarbawa Ya Ja Kunnen Rundunar Soji

Shugaban Kungiyar Tsagerun Yarbawa masu kyamatar ‘yan Arewa Mista Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya ja kunnen jami’an tsaro a kan bibiyar Yarbawa mafarauta ko masu gadi dake amfani da manyan bindigogi wajen ayyukan su.

Sunday Igboho ya sanar da hakan ne a wani faifan bidiyo da tsohon Ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya wallafa a shafin sa na Twitter.

Shugaban Tsagerun Yarbawan ya ce, “Muna farin ciki da umarnin halaka duk makiyayin da aka kama da AK-47 da shugaban kasa ya bada. Duniya za ta san abinda makiyaya ke yi da kuma wanda suka yi. Muna farin ciki da umarnin shugaban kasa.

“Mun ga amfanin duk abubuwan da muka dinga fadi. Makiyayan nan na amfani da Ak-47 ne domin garkuwa da mutane, fashi, fyade da kuma neman fitina, amma mun godewa Ubangiji da maganganunmu suka yi amfani.

“Abinda nake so cewa shine, ‘yan sanda, jami’an hukumar tsaro ta farin kaya da sojoji, gwamnati ta bada umarnin harbesu a take idan an kama su da Ak-47 suna barna, muna so ku san cewa Sheikh Gumi ya nuna muku inda makiyayan nan suke.

“Bai ce ku nuna bangaranci ba. Bai ce ku je kasar Yarabawa ko ta Ibo ku fara kashe jama’a ba. “Kada ku ga mutum da bindiga a cikin ‘yan uwana Yarabawa saboda tsaro suke amfani da su ku kuma ku harbesu. Kada ku kuskura ku fara hakan.

“Kada daga kun ga mutum da bindiga ku manna masa sharri ku halaka shi.Muna rokon ku da ku kasance masu adalci.” Idan an ki ji to ba za’a ƙi gani ba!

Labarai Makamanta