Shugaban Talabijin Na LIBERTY Ya Taya Tinubu Murnar Ranar Haihuwa

Shugaban Kamfanin Attar Communication mai gidajen Talabijin da Rediyo na Liberty Ahmad Tijjani Ramalan ya taya jigon siyasar APC Bola Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwarshi shekara 69.

A cikin wata takardar sanarwa da ya fitar wadda aka rarraba wa manema labarai a birnin tarayya Abuja, Tijjani Ramalan ya bayyana Tinubu a matsayin tsayayyen mutum mai akidar siyasa ta kwarai.

“A fili yake Bola Tinubu dan siyasa ne kuma jagora abin koyi, wanda salon tafiyar da al’amuran shi suka tabbatar da kirarin da ake yi mishi na Jagaban Ƙasa.

Ramalan ya ƙara da cewar Tinubu ya zama babban jigo kuma abin koyi a ‘yan siyasar Najeriya wadanda damuwar cigaban ƙasa ita ce damuwarsu, ba kallon wani bangare ba.

Ya yi addu’ar kara samun lafiya da tsawon kwana ga jigon siyasar da addu’ar samun nasara a bukatun shi da yake nema.

Labarai Makamanta