Shugaban Masu Bautar Shaidan Mai Mata 57 Ya Yi Mummunar Cikawa

Sarkin masu bautar shaiɗan’ na Najeriya Simon Odo wanda shi ne mutumin da ya auri mata 57 ya rasu yana da shekara 74.

Ɗansa Uchenna Odo ne ya tabbatar wa BBC da lamarin inda ya ce mahaifinsa ya rasu ne a ranar Talata da dare bayan gajeruwar rashin lafiya.

Simon Odo wanda asalinsa ɗan Jihar Enugu ne ya shahara ne a kudancin Najeriya a harkar bokanci da bautar shaiɗanu.

A yayin wata hira da BBC a bara, marigayin ya ce ya auri mata 57 kuma bai san iyakar ƴaƴan da matansa suka haifa ba haka ma jikokinsa.

Ya kuma bayyana wa BBC cewa ya gaji bautar shaiɗan ne daga iyayensa da kakanni.

Labarai Makamanta