Shugaban Majalisar Koli Ta Shari’ar Musulunci Datti Ahmad Ya Rasu

Wasu rahotanni daga jihar Kano sun bayyana cewa Allah ya yiwa shugaban majalisar ƙoli ta shari’ar Musulunci, Dr. Ibrahim Datti Ahmad, rasuwa.

Datti Ahmda, wanda a shekarun baya ya yi yunƙurin shiga tsakani domin tattaunawar tsakanin jami’an gwamnatin kasar nan da kuma ‘yan kungiyar nan ta Jama’atu Ahlis Sunnati Lidda Awati wal Jihad, da aka fi sani da Boko Haram, ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya.

Za a kuma a yi jana’izar sa a masallacin Al -furqan da ke birnin Kano, da misalin ƙarfe 10 na safiyar yau Alhamis.

Labarai Makamanta