Shugaban Liberty Talabijin Ya Karbi Lambar Yabo Ta Zama Gagara Badau

Jaridar yanar gizo ta politics Today ta karrama Shugaban rukunin kanfanin ATAR communications, mamalakin gidan talbijin da rediyo na liberty da jaridar voice of liberty (Muryar yanci) Dr Ahmed Tijjani ramalan da lanbar yabo na Gagara Badau na shekarar 2021 saboda gudunmuwar da ya kawo a harkar yada labarai a yankin arewa da kasa baki daya.

Karramawar da akayi wa dr Ahmed Tijjani Ramalan ya biyo bayan cigaban da ya kawo a yankin arewacin kasar nan da Najeriya baki daya. Mun duba yadda yake tafiyar da gidajen radio, talbijin da jarida a arewa duk da kalubalen da ake fuskanta a wannan harkar ta yada labarai musamman a yankin mu na arewa. Sannan an duba yadda yaba daruruwan matasa ayyukan yi ta fannoni da dama da kawo shirye shirye masu fadakar da al’umma. Wannan na cikin dalilian da yasa muka karrama Dr Ramalan,” Inji Danbatta

Hakan na kunshe ne a jawabin da babban editan jaridar Nasir Danbatta ya fitar a ranar asabar ga manema labarai a jim kadan bayan karrama Dr Ahmed Tijjani Ramalan.

Dr Ahmed Tijjani Ramalan ya sadaukar da wannan karramawar da akai masa ga illahirin ma’aikatansa, domin a cewar Dr Ramalan “aikin da sukeyi ba dare ba rana shiya kawo Masa wannan nasarar.kuma wannan karramawar da sukai Masa zai kara masa kwarin gwuiwa wurin ganin an samu cigaba ta kowani fanni.

Jaridar Politics today ta bayyana Dr Ahmed Tijjani Ramalan a matsayin Gagara Badau a masu tafiyar da aikin watsa labarai na arewacin kasar nan, da Kuma wani jigo abin kwaikwayo musamman a fannin aikin jarida. Karramawar na daya daga cikin abubuwan da suka shirya a bikin cikar jaridar Politics today shekara biyu da kafuwa.

Labarai Makamanta