Shugaban Kasar Ghana Ya La’anci Masu Auren Jinsi

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya yi tir gami da Allah wadai da masu hanƙoron auren jinsi, inda ya bayyana cewa auren jinsi ba zai taba faruwa ba a karkashin mulkin sa har abada ba.

Ya fadi haka ne a wani taron coci da aka yi a Mampong ranar Asabar, 27 ga watan Fabrairu cikin dinbin jama’a.

”Na fadi hakan a baya, kuma bari na sake jaddada cewa ba a karkashin Shugabancin Nana Akufo-Addo za a halatta auren jinsi a Ghana ba.

“Ba zai taba faruwa ba. Bari in maimaita; ba zai taba faruwa ba,” in ji shi cikin tsananin fushi.

Bayanin nasa ya biyo bayan rufe wani ofishin LGBTQ + wanda aka bude kwanan nan a Accra, babban birnin kasar ta Ghana.

Batun auren jinsi ya ƙara samun karfafuwa a duniya tun bayan lashe zabe da sabon Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi, inda gwamnatin sabon Shugaban ta fito ƙarara ta nuna goyon bayan ta ga masu auren jinsi.

Labarai Makamanta